Wannan shi ne jigon babban taron kungiyar a kasuwar shanu ta Maliya da ke jihar Nasarawa.
Miyetti Allah daya daga manyan kungiyoyin makiyaya ta ce makarantun makiyaya ba sa wadatarwa wajen samar da ilimi don karancin malamai da kayan aiki.
Shugaban kungiyar Bello Bodejo Lamido Fulbe ya nesanta Fulani makiyaya daga taurin kai sai dai rashin fahimta; inda ya koka da abun da ya zayyana kudin goro da a ke yi wa Fulanin daji a zarmewa doka.
Kazalika Bello Bodejo ya ce sun shirya kafa kungiyar sintiri da za ta rika aiki da jami'an tsaro don zakulo miyagu don raba aya da tsakuwa.
Uwar kungiyar Hajiya A’ishatu Bala Muhammad Kauran Bauchi ta ce tsayin daka kan ilimi ne za su cigaba da yi.
Makiyaya daga sassa daban-daban musamman na arewacin Najeriya sun halarci taron da niyyar mika wuya ga ilimin addini da na zamani.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5