Lamarin ya shafi kauyuka uku da suka hada da Tattara Mada, Anguwan Barau, da Kiwiyi, ya kuma haddasa kone-konen gidaje da akan tilas gwamman mutane suka gujewa gidajensu.
Shugaban kungiyar Kristoci ta CAN a karamar hukumar Kokona, Rabaran Bitrus Kaya, yace rikicin ya fara ne saboda sarar bishiyar mangoro, don bai wa dabbobi abinci.
A gefe guda kuwa, shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Nasarawa, Bala Muahammad Dabo, ya ja hankalin bangarorin biyu wadanda a baya basu taba samun tashin hankali ba, da su kai zuciya nesa.
Duk kokarin ji daga bakin ‘yan sandan jihar Nasarawa, ya ci tura, domin kakakin rundunar, DSP Ramhan Nansel bai maida martani ba.
Tun bayan kammala zabuka ne dai hare-haren ‘yan bindiga da rikicin makiyaya da manoma suka fara kunno kai a jihohin Binuwai, Nasarawa, da Filato, lamarin da yayi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi.
Saurari rahoton Zainab Babaji: