ICC: Afirka Ta Kudu Ta Yi Maraba Da Mika Bukatar Kama Netanyahu, Shugaban Hamas

Kotun Kararrakin

Fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta bayyana a ranar Litinin cewa ta yi marhabin da sanarwar da mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC ya yi akan shugabannin Isra’ila da Hamas.

WASHINGTON, D. C. - ICC ta bukaci sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ne da babban hafsan tsaronsa da kuma shugabannin Hamas uku bisa zargin aikata laifukan yaki.

ICC - Karim Khan

A wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya fitar, ya ce "dole ne a yi amfani da dokar bisa ka'ida kuma daidai domin kiyaye dokokin kasa da kasa, da tabbatar da bin diddigin wadanda suka aikata munanan laifuka da kuma kare hakkin wadanda abin ya shafa."

Cyril Ramaphosa

Kasar Afirka ta Kudu wadda ke kan gaba wajen fafutukar kare muradun Falasdinawa, da ma ta kai karar Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa tana zarginta da aikata kisan kiyashi, wanda ta musanta.

Netanyahu

Shugabannin Isra'ila da Hamas sun yi watsi da zargin aikata laifukan yaki, kuma wakilan bangarorin biyu sun soki matakin da mai gabatar da kara ya dauka.

-AP