A zaman da ta yi a yau Alhamis a Abuja, kotun ta sanar cewa, masu korafi a wannan shara’a da sunan gwamnatin Nijar game da matakan da ECOWAS ta dauka bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli ba su da hurumin shigar da kara a gabanta kasancewar sun hau karaga ne ta hanyar da ta saba wa doka saboda haka kotun ta kori wannan kara.
Kotun ta kuma kori wata karar ta daban da wasu kamfanoni da masana’antun Nijar suka shigar kan jerin takunkumin ECOWAS. Tana mai cewa ba wani bambanci tsakanin nasu korafin da wanda hukumomin Nijar suka gabatar saboda haka layinsu daya a idanun doka.
Jami’in kula da harakokin sadarwa a fadar Fira Minstan Nijar Ibrahim Hamidou yace, da ma sun san za a rina a bisa la’akari da yadda dalilan siyasa suka rinjayi sha’anin doka a lamuran kotun.
Da ma dai masana sun ayyana cewa, hanyar diflomasiya ita ce hanya mafi a’ala wajen warware wannan dambarwa domin idan aka nazarci yarjeniyoyin da kasashen Yammacin Afrika suka saka wa hannu, za a iya gane cewa bi ta hanyar shara’a mataki ne mai cike da sarkakiya.
A ranar 30 ga watan Yulin 2023 ne taron shugabanin kasashen kungiyar CEDEAO da ya gudana a Abuja ya yanke shawarar kakaba jerin takunkumin kan Nijar a sanadiyar juyin mulkin da soja suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum matakin da ya matukar shafi rayuwar al’umma, mafari kenan hukumomin mulkin soja suka nufi kotun ECOWAS domin ankarar da ita rashin halaccin wannan mataki.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5