Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar ya ce ba za a fara tattaunawa kan takunkuman da aka sakawa Jamhuriyar Nijar ba har sai idan gwamnatin sojin kasar ta saki Shugaba Mohamed Bazoum.
A ranar 26 ga watan Yuli sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar suka hambarar da Bazoum tare da tsare shi da iyalansa.
Hakan ya sa kungiyar ECOWAS ta kakabawa kasar takunkumin ta kuma nemi sojojin da su saki Bazoum tare da mayar da shi kan karagar mulki, lamarin da ya citura, duk da barazanar da ECOWAS ta yi na daukan matakin soji.
Yayin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels TV a gefen taron yanayi a Dubai, Tuggar ya ce sun riga sun fadawa sojojin sharuddan da suke so a aiwatar idan har suna so a dage takunkumin.
Al’umar kasar ta Nijar sun shiga matsanancin halin rayuwa tun bayan da Najeriya da wasu kasashen yammacin Afirka suka rufe kan iyakokinsu da kasar bisa umarnin kungiyar ta ECOWAS.
Lamarin ya fi kamari bayan da Najeriya ta rufe iyakokinta da kasar duba da cewa akwai kwakkwarar cinikayya tsakanin kasashen biyu.
“Mun riga mun bayyana komai karara. Abin da muke cewa shi ne su saki Shugaba Bazoum saboda ya ya bar kasar ta Nijar, ya koma wata kasa da aka amince, sannan sai mu fara magana kan takunkumian da aka saka.” Tuggar ya ce.
Ministan ya kara da cewa, wannan mataki da aka dauka na kakaba takunkumin, matsaya ce ta ECOWAS ba Najeriya ba.
Tuggar ya kara da cewa har yanzu suna ci gaba da tattaunawa da hukukomin sojin na Nijar yana mai jaddada cewa kofofin ECOWAS a bude suke a ko da yaushe idan sojojin suna so a tattauna.
A cewar Tuggar, yanzu komai ya rage ga su sojojin ne domin ECOWAS ta riga ta bayyana matsayarta.
Minisitan ya kuma kore zargin da wasu ke yi cewa wasu kasashe ne ke fadawa Najeriya abin da za ta yi kan lamarin na Nijar.
“Babu rashin jituwa tsakanin Najeriya da Nijar. ‘Yan Najeriya da Nijar ‘yan uwa juna ne, babu sabani tsakaninmu. Kada wani ya rude ka cewa wasu kasashe ne suke fadawa Najeriya abin da za ta yi.” Channels TV ya ruwaito Ministan yana fada.
Dandalin Mu Tattauna