Hukumomin Shiga Tsakanin Jama'ar Kasashen UEMOA Sun Fara Taron Duba Gudunmuwar Da Zasu Bada Wajen Magance Rigingimu

UEMOA

Shugabanin hukumomin shiga Tsakani daga kasashen yammacin Afrika mambobin kungiyar UEMOA sun fara gudanar da taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer domin duba gudunmuwar da zasu bayar wajen warware rigingimun da ake fama da su a kasashen yankin.

Ganin yadda rikice rikice ke kara yaduwa a ‘yan shekarun nan a sassan Afrika ya sa kungiyar kasashen Afrika ta yamma renon Faransa kiran wannan taro domin nazari akan kalubalen da ke gaban gwamnatocin wadannan kasashe.

A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Moustapha Kadi Oumani s darektan ofishin babban jami’in hukumar shiga tsakanin ta kasar Nijer Mediature Nationale, ya bayyana cewa, "matsaloli suna da yawa, matsalar tsaro ita ce kan gaba da ta dami al'umma, sai kuma matsalar zamantakewar makiyaya da manoma, matsalolin dai suna dayawa kuma sun game duniya, dole ne sai an hada kai don a sami zaman lafiya"

Dabaibayin dake tattare da tsarin aikin hukumomin shiga tsakani a mafi yawancin kasashen Afrika wani abu ne dake bukatar dubawa, lura da haka ya sa Burkina Faso sakarwa hukumar shiga tsakanin kasarta ragama inji shugabar wannan hukuma, Madame Sanou Fatimata.

Tace mu a Burkina Faso hukumar shiga Tsakani na da damar daukan matakan riga kafi idan ta gano alamun wasu abubuwan dake kokarin haddasa rikici a tsakanin al’umma abinda ke taimakawa sosai wajen kwantar da wutar rikici kuma akai akai mutane ke kai koke kokensu a wannan hukuma don sasantawa kuma kamar yadda aka sani mu a nan Afrika mutane sun fi ganinta a warware rikici cikin ruwan sanyi a maimakon a yi ta kai da kawo a kotu.

Tsaikon da ake fuskanta wajen gudanar da aikin shiga tsakani da rashin kayan aiki irin na zamani, wani bangare ne na batutuwan da wannan zama zai zanta akansu.

Kafin wannan zama kwararru a fannin dubarun sulhunta rigingimu da wanzarda zaman lafiya sun rubuta littatafai 2 masu dauke da shawarwarin suke ganin idan taron na yau ya yi na’am da su jama’ar kasashen nan 8 na kungiyar UEMOA wato Nijer Mali Burkina Faso Togo Benin Senegal cote d’ivoire da Guinee Bissau zasu mori aiyukan hukumomin shiga tsakani a duk lokacin da irin wannan bukata ta taso.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Shiga Tsakanin Jama'ar Kasashen UEMOA Sun Fara Taro Duba Gudunmowar Da Zasu Bada Wajen Magance Rigingimu