A watan Maris din dake tafe ne Firai Ministan Nijer Ouhoumoudou Mahamadou zai gabatar wa majalisar dokokin kasa hujjojin gwmantinsa a hukunce domin neman yardar ‘yan majalisa akan matakin girke sojojin rundunar Takuba da Barkhane a kasar wanda ya biyo bayan yanayin tsamin dangantaka a tsakanin kasashen Mali da Faransa.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan majalisar dokokin kasa daga bangaren masu rinjaye Kalla Moutari tattauna wannan batu a majalisance hanya ce ta tantance matsayin gwamnatin a idon wakilan talakkawa.
Sai dai shugaban jam’iyar ORDN Tauraruwa ta kawancen jam’iyun hamayya Malan Maman Sani Adamou na ganin tunkarar talakkawa kai tsaye da wannan batu ita ce hanya mafi dacewa wajen warware wannan dambarwa.
Rashin hukuma a kusan kashi 2 daga cikin 3 na fadin kasar Mali ya yi sanadin lalacewar sh’anin tsaro a ‘yan shekarun nan a jihohin Tilabery da Tahoua saboda haka mahukuntan Nijer ke dauka zuwan sojojin takuba da na Barkhane a matsayin matakin rufewa ‘yan ta’addan hanyoyin shiga kasar.
To amma ‘yan adawa na kallon wannan mataki da wata fuska ta daban…suna ganin dakarun Faransan sun saba duk inda suke babu wani wanda zai tambayesu abun da su ke yi, ko da sojojin faransan sun yi barazana ko barna, ba mai tambayarsu ko a hukunta su ba, sai dai hukumar Nijar ta dauki nauyin hakan.
Labarin ficewar wadanan dakaru zuwa Nijer sakamakon tankiyar diflomasiyar da ta barke tsakanin Mali da Faransa wanda ainihi aka fara jinsa daga bakin shugaba Emmanuel Macron abu ne da masana ke kallonsa tamkar wani yunkurin da zai fake da shi don karawa kansa kwarjini a wajen jama’ar kasar wadanda zasu halarci runfunan zabe a watan Afrilun dake tafe.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: