Harin na baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka kai ya hada da daukar wata budurwa ‘yar makaranta da ke ajin sakandre.
Wasu daga cikin garin sun shaida wa Muryar Amurka cewa muddin dare ya yi sun shiga fargaba saboda tunanin idan sun kwanta barci ‘yan bindiga za su kai masu hari su karshe da ‘ya’yansu.
Wani mazaunin garin ya ce akwai daji dake bayan garin wanda ya sa ‘yan bindigan suke da wuyan kamuwa. Ya ce da zaran jam’ian tsaro sun bisu, sai su fada cikin daji wanda yake da girma da kuma zurfi, dalilin da ya sa ke nan yake da wuyan kama ‘yan bindigan.
Ya kara da cewa akwai sojoji guda 15 ne kacal, amm da da zu samu karin kamar sojoji 60, a zagaye masu garin suna ganin abin zai yi masu sauki. Saboda haka ya ce suna rokon gwamnati don Allah ta taimaka masu.
A harin da ‘yan bindigan suka kai har suka sace wata budurwa mai shekara 17, mahaifinta ya ce sun yi ta jani-in-jaka da ‘yan bindigan, bayan da ya dauki adda, amma sai suka haura cikin gidansa inda suka dauke masa ‘yarsa.
A yanzu haka dai wannan matsala ta hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da daukan hankulan jama’ar Madarunfa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mansour Sani: