A bisa al’ada ayyukan kona miyagun kwayoyi abu ne da ake gudanarwa a ranar yaki da fataucin miyagun kwayoyi da ake bikin a kowace ranar 26 ga watan Yuni, to amma ganin girman cafkar da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta yi a wannan karon ya sa hukumomi neman izinin kotu domin kona hodar iblis din kg 214 da aka kama a ranar 3 ga watan Janairun 2022 a hannun magajin garin Fachi na yankin Agadez.
Domin kawar da dukkan wasu shakku daga kawunan jama’a, jami’an tsaron hukumar OCRTIS sun fara ne da aikin tantance darajar wannan haja da a can farko aka bayyana cewa cocaine ce gangariya.
Bayan kammala aikin gwaje-gwaje daga bisani an konata akan idon ministan shari’a da takwaransa na cikin gida, a idon ‘yan jarida da jam’ian kungiyoyin fararen hula da aka gayyato takanas domin zama shaidun wannan aiki da ya gudana a birnin Yamai.
Fataucin miyagun kwayoyi wani abu ne da aka yi amannar cewa ya taka rawa sosai wajen tabarbarewar sha’anin tsaro a ‘yan shekarun nan saboda yadda ake amfani da kudaden shigarta wajen daukar dawainiyar kungiyoyin ta’addancin da suka addabi wannan yanki.
Mafari kenan masu wannan haramtaciyar sana’a suka dage wajen shigo da tsadaddiyarta da nufin batar da ita a Nijer, ko kuma su ratsa kasar akan hanyarsu ta zuwa wasu kasashe na dabam, inji Ministan shari’a Mohamed Ikta wanda ya jagoranci wannan aiki.
Ko a jajibirin wannan aiki na kona hodar iblis hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi OCRTOS ta gabatar da wani dan Najeriya da ta ce ta kama a filin jirgin saman Diori Hamani, lokacin da yake kokarin aika wani na’unin kwayar Metamphetamine kg 1 da kusan rabi zuwa kasar Australia.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5