Hukumomin Nijer Sun Bayyana Shirin Zuba Kudin Tallafin Mai Don Shigo Da Iskar Gas Daga Ketare

Matatar man 'Nord Stream 1'

A yayin da matatar man SORAZ ke shirin dakatar da aiki don yin gyare gyare, Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta bada sanarwar daukar matakan riga kafi da nufin kauce wa karancin iskar gas a tsawon wannan lokaci. A saboda haka ta gargadi masu sana'ar iskar gas su mutunta tsarin farashin da aka kayyade.

NIAMEY, NIGER - A Sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, ministocin harkokin kasuwanci, man fetur da na kudi a Nijer sun bayyana cewa kamfanin dillancin man SONIDEP zai rika shigo da iskar gas daga waje domin sayar da shi akan farashin da aka saba sayarwa, duk da barazanar da sha’anin makamashi ke fuskanta a kasashe da dama sanadiyar yakin Rasha a Ukraine.

Shugaban kungiyar CODDAE mai kare hakkin jama’a a fannin makamashi Alhaji Moustapha Kadi Oumani, ya yaba da matakin gwamnatin koda yake ya ce sai an dauki matakan zuba ido saboda wasu zasu yi amfani da wannan damar don alfanun kansu.

Domin toshe hanyoyin fasakwabrin iskar gas a tsawon wannan lokaci, hukumomin sun ce zasu rufe illahirin tashoshin ajiyar iskar gas da ke kan iyaka daga ranar farkon soma ayyukan gyare gyaren matatar ta SORAZ har zuwa karshe, wato daga ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar 2022 zuwa 30 ga watan Nuwamba. Shugaban kungiyar kamfanonin dillancin iskar gas Mahmoud Ali shi ma ya yaba da wannan mataki amma ya ce ya kamata gwamnati ta kara a kan wannan kokari.

A galibin wurare akan sayar da kg 12 na iskar gas akan 5000 F CFA ko ma fiye da haka, alhali gwamnati ta kayyade farashin kg 12 akan 3750 F. A saboda haka ministocin da ke kula da wannan harka suka gargadi masu wannan sana’a da su bi doka.

A cewar wani jigo a kungiyar SYNAREG ta masu kasuwancin iskar gas Oumar Alhaji Mamadou, wannan mataki na bukatar dubawa. Ya ce a birnin Yamai kadai akwai matasa sama da 4,500 da ke sana’ar saida gas, idan gwamnati ta dauki wannan mataki kashi 99.9 cikin 100 na masu sana’ar ba zasu iya yi ba.

A can baya, kamfanin dillancin mai kan sayi kowace litar iskar gas akan 120 F CFA a matatar SORAZ don sayar da shi ga kamfanoni akan 128 F, a yayin da farashin lita ke 1070 na CFA a kasuwannin kasashen waje don sakar da shi ga ‘yan kasuwa akan 128 F, a matsayin wani bangare na matakan takaita yawan masu amfani da itace a matsayin makamashi.

Saurari cikakken rahoton Souley Mumuni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Nijer Sun Bayyana Shirin Zuba Kudin Tallafin Mai Don Shigo Da Iskar Gas Daga Ketare