Sai dai hauhawar farashin kayayyakin da kuma abubuwan da ke faruwa a kasuwannin danyen mai na kasa da kasa da faduwar darajar cedi su ne su ka haifar da wannan tsadar iskar Gas a Ghana, yayin da masana ke ganin gwanmanti ba za ta cimma wannan buri ba.
Mallam Faruk ya ce tunda yayi aure sama da shekara 6 shi ke zuwa sayen iskar gas ma iyalinsa, sai dai yanzu ya koma sayen gawayi sabida tsadar gas a Ghana.
Ita kuwa Hajiya Zati ta ce tana amfani da gas da gawayi wajen yin girki wanda a da ba haka ba ne.
Su kuwa masu saida gawayi a Ghana sun nuna jin dadinsu na yadda kasuwar gawayi ke tashi .
A'isha mai gawayi ta ce yanzu tana saida buhu hamsin cikin kwana uku.
Nanaba Osei Tutu Collins mai saida iskar gas ya ce. “Kamar yadda muke magana yanzu, kasuwar gas tana raguwa. Mun rungumi sabuwar hanyar sayar da ita ga masu saye da sayarwa ta yadda za su iya sayan kowane adadin da za su iya. A da muna sai da metrik ton 29,000 zuwa 30,000 a cikin wata daya a duk fadin kasar Ghana amma yanzu ya ragu zuwa metric tonne 16,000 a wata daya.”
Shi kuwa Daraktan Cibiyar Makamashi ta Brew-Hammond a Jami’ar KNUST, Farfesa Francis Kemausuor ya ce, da zarar mutane sun koma yin amfani da gawayi da itace kuma muna cikin zamanin da dajinmu ke bushewa, hakan zai yi tasiri wajen samun sauye-sauye da dama ga ababen shuki da dabbobi da kuma albarkatun daji.
An kara farashin iskar gas aƙalla kashi 44 cikin ɗari a tsakanin watan Janairu da Agusta, 2022.
Saurari rahoton Hauwa Abdulkadir: