AGADEZ, NIGER - Kayan miyagun kwayoyin da aka kona sun hada da tabar Wiwi da Cocaïne da kuma Tramadol da dai sauransu.
Hukumomi a jihar Agadas ta Jamhuriyar Nijar sun nuna damuwa dagane da yadda safarar miyagun kwayoyi ke nema samun gurin so sai a jihar, da kuma yadda ta’ammali da miyagun kwayoyin ke zama karfen kafa a tsaknin al’umma.
Hukumomin su ce ya zama wajibi a yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan mummunar dabi’a domin samar da al’umma ta gari.
A wani na kokarin tabbatar da hakan, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta gudanar da bikin kona kimanin tan 1.5 na kayan shaye-shaye a gaban hukumomin jihar Agadas, karkashin Henri Marthin Muktar babban alkali na jihar Agadas.
Tuni dai al’ummar garin suka bayyana jin dadinsu game da yadda ake samun nasara akan masu safarar miyagun kwayoyi.
Kungiyoyin farar hula sun jinjinawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, inda hukumomi suka sha alwashin baiwa hukumar duk irin goyan bayan da take bukata domin kawar da wannan mummunar dabi’a a kasa baki daya.
-Hamid Mahmud