Hukumomin Nijar sun haramta hakar ma'adinai a arewacin kasar da ke yammacin Afirka.
‘Yan kasashen ketare musanman kasashen China da kuma Sudan dake aikin hakar zinaren ba bisa ka’ida ba, da kuma gurbata muhalli na daga cikin dalillan da suka sanya mahukunta daukar wannan matakin domin kawo sabbin tsare-tsare a wuraren
Masu fashin baki irin su Adourahamane Ali na ganin matakin ba zai rasa nasaba da yadda kasar Rasha ke kara tasiri a tsakanin kasashen Sahel ba, da kuma yadda Rasha ke kara sha’awar son hakar ma’adinai a kasar.
Tuni dai kungiyoyin matasa ke fargabar abubuwan da za su biyo baya, ganin yadda dubban matasa ne ke aikin hakar ma’adinan zinaren, kamar yadda Ousmane Bianou shugaban wata kungiyar matasa a Agadaz ya bayyana mana.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5