Kamfanin Orano ya bayyana cewa akwai matukar wahala ya ci gaba da aikin hako uranuim a wannan kasa dake yammacin Afirka da sojoji suke mulki.
A cikin wata sanarwa da kanfanin Orano, da ya shahara kan harkokin nukiliya a duniya kuma mallakin kasar Faransa, ya bayyana cewa ya dakatar da aikinsa na samar da karfen uranuim a jihar Agadas dake arewacin Nijar.
Kamfanin ya nuna cewa ba zai ci gaba da wannan aikin ba duba da irin matsalolin da yake fuskanta a Nijar.
Yanayin da kamfanin yake ciki na rashin fitar da karfen uranuim wanda yanzu haka akwai kimanin ton 1050 dake ajiye tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara sakamakon tsamin dangantakar dake tsakanin mahukuntan Nijar da kasar Faransa da kuma matsalolin kudi da kanfanin yake fuskanta yasa kanfanin tsayar da aikin hakar uranuim a Nijar.
A cewar Orano duk da irin kokarin da kanfanin yake yi domin daidaita al’amuran cikin ruwan sanyi tsakaninsa da hukumomin mulkin sojan kasar Nijar domin samun takardun izinin fitar da uranuim lamarin ya ci tura.
Matakin kamfanin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kamfanin kasar Canada, Global Atomic ya sanar da shirinsa na soma aikin hako ma'adinan uranuim a arewacin Nijar a 2026.
Tuni kungiyoyin fararen hula suka fusata dangane da wannan matakin na kanfanin Orano.
Malam Mohamed Ali dake aikin sanya ido kan yadda ake hako ma’adinai a Agadas na ganin akwai bukatar gwamnatin Nijar ta baiwa wasu kasashen damar hakar ma’adinan.
Masu fashin baki irinsu Abdourahmane Dikko na fassara wannan matakin da wani yunkuri na neman tilastawa gwamnatin Nijar sassautowa daga kudurori da ta dauka.
A cikin watan Yuni ne gwamnatin Nijar ta janye lasisin hakar uranuim na iImouraren ga kanfanin na Orano.
To saidai a cikin wata sanarwa da kanfanin dake kula da ma’adinai a Nijar na Sopamine ya fitar ya bayyana takaicin sa game da wannan matakin na Orano da kuma sabawa yarjejeniyoyin dake tsakanin Nijar da kamfanin.
Ga dai sautin rahoton Hamid Mahmod daga Agadez:
Dandalin Mu Tattauna