Hukumomi a Najeriya, sun amince da kafa kungiyar tsaro ta Amotekun da wasu jihohin kudu maso yammacin kasar suka yi.
A farkon watan nan, jihohin Ondo, Osun, Ogun, Ekiti, Oyo da Legas, suka kafa wata rundunar tsaron ta Amotekun.
Manufarsu kamar yadda suka fada, ita ce, su yaki matsalar tsaro a yankin.
Sai dai Babban Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, ya fito a kwanin baya ya ayyana matakin a matsayin abin da ya "sabawa doka."
Hakazalika, lamarin ya janyo muhawara a tsakanin jama'ar kasar, inda yayin da wasu ke goyon bayan matakin wasu kuwa akasin hakan suke nunawa.
Matakin amincewa da kungiyar tsaron, ya biyo bayan wata ganawa da gwamnonin suka yi da mataimakin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo a ranar Alhamis.
Zaman ya hada har da Atoni Janar Malami da kuma Sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar.
Mai Magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, ya ce gwamnonin ne suka nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan batu da ke ci gaba da janyo muhawara.
“Zama ya yi ma’ana kana an samu fahimtar juna kan mataki na gaba game da batun” Akande ya ce cikin wata sanarwar da ya fitar.
Sai dai masana tsaro a Najeriya irinsu, Aliko El Rashid Harun na nuna fargabrsu kan wannan mataki da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
A cewar shi, gwamnati ta yi amai ta lashe abin da ya kuma ce mai yiwuwa ne nan da ‘yan watanni kadan a samu rikici tsakanin jami’an tsaron tarayya da na jihohin da aka kafa karkashin rundunar Amotekun.
Ana su bangaren, masana shari'a irinsu Barr. Yakubu Sale Bawa, na ganin kafa wannan rundunar tsaron bai sabawa dokokin kasa ba.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina kan wannan batu:
Your browser doesn’t support HTML5