Hukumar da ke dakile yaduwar cuttuttuka a Najeriya ta NCDC, ta ce an saka jami’an kiwon da ke filayen jirage da hanyoyin shiga kasar cikin shirin ko-ta-kwana.
Matakin na zuwa ne bayan bullar sabuwar cutar Coronavirus a kasar China.
“Za a iya bincikar lafiyar matafiya daga yankin Wuhan zuwa Najeriya yayin da suka isa kasar, a ga ko suna da alamun cutar.” Wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar ta ce.
Hukumomin na Najeriya, sun kuma ba jama’ar kasar shawarar su “kwantar da hankulansu.”
A jiya Laraba, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta gudanar da wani taron gaggawa domin tattauna batun bullar cutar.
Bayanai sun yi nuni da cewa, cutar ta fi yaduwa ne a birnin Wuhan da ke tsakiyar kasar ta China.
Kwayoyin cutar na kuma iya rikidewa su koma na cutar nan mai toshe hanyoyin numfashi ta SARS.
Ya zuwa yanzu, hukumomi a Beijing sun tabbatar da mutuwar mutum 17 sannan wasu sama da 400 sun kamu da cutar.
Mafi aksarinsu mutane ne da suka manyanta.
Baya ga kasar ta China, an samu bullar cutar a wasu daidaiku kasashe da suka hada da Thailand, Japan, Tarayyar Korea da kuma Amurka.
Dukkan wadanda aka samu da cutar a wadannan kasashe, an samu alaka ta tafiya da suka yi zuwa wasu yankunan China.