A Najeriya, yayin da babbar kotun koli ta kasar ta ayyana gobe Litinin a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin kararrakin zabe na wasu gwamnonin jihohi da aka gabatar mata, a gefe guda kuma jam’iyyun siyasa sun yi kira ga magoya bayansu da su kaurace wa duk wani abun da zai kawo tashin-tashina a dangane da irin hukuncin da kotun kolin za ta bayyana.
A Jihar Bauchi, akwai shari’a tsakanin jam’iyyar PDP da kuma jam’iyyar APC wadda ta ke kalubalantar nasarar lashe zaben da jam’iyyar PDPta yi a zaben shekarar bara. A dangane da hakan jigo a jam’iyar APC ya shawarci magoya bayansu da su kasance masu bin doka da kuma umurnin kotu.
Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi shi ma ya bukaci zaman lafiya a dangane da irin sakamakon da zai bayyana.
Gamayyar kungiyoyin farar hula ta gudanar da taro a sakatariyar ‘yan jarida a Bauchi, domin yin kira ga matasa da kuma ‘yan siyasa, dangane da muhimmancin zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad.
Facebook Forum