A Najeriya, cacar baki ta barke tsakanin rundunar sojin kasar da Tarayyar Turai game da koma bayan da ake samu da 'yan ta'addan Boko Haram.
Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta ce yakin da ake gwabzawa da mayakan
Boko Haram ya ki karewa, sai dai ma koma baya da ake fuskanta, ganin yadda abubuwa suke faruwa a 'yan makonnin nan.
Majalisar ta Turai ta ce yankan rago da aka yiwa wasu mutane 11 da 'yan ta'addan ke garkuwa dasu, da harin da mayakan Boko Haram suka kaiwa babban kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, da karuwar hare hare a yankin, duk wasu alamu ne da ke nuni da kara tabarbarewar tsaro a kasar.
Amma cikin wani martani na gaggawa, Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar
sojin kasar Tukur Buratai, ya jaddada cewa sojojin na
samun nasara a fafatawar da su ke yi da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas da ma sauran sassan kasar.
Daga bisani Janar Buratai ya gargadi duk masu kokarin ganin sun ruruta
wutar rikici a Najeriya, ya kirasu "makiyan Najeriya," ya kuma ce 'yan Najeriya su yi hattara da su.
A saurari rahoto cikin sauti.
Facebook Forum