A bayannan da ya yi wa manema labarai cikin mintoci kalilan, Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine ya fara ne da zayyana yadda aka saka ranakun zama a na dagewa har sau biyu kafin daga bisani hukumomin mulkin sojan na Nijar da shugabanin kungiyar ECOWAS su ka cimma daidaito kan ranar 25 ga watan Janairun 2025 a matsayin wace za a fuskanci juna.
Sai dai an shafe tsawon wannan rana amma tawwagar jami'an kungiyar ba ta shigo ba in ban da Ministan Harakokin Wajen Togo, Robert Dussey, da ya sauka birnin Yamai inji Fira Minista Zeine.
Sai dai yunkurin jin ta bakin Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey wanda ya halarci taron maneman labaran da Firai Minista Lamine Zeinab ya kira ya ci tura.
Shugaban gwamantin rikon kwaryar ta Nijar ya bayyana wa manema labarai cewa bai zama dole ba ministan na Togo ya yi magana.
Rashin samun izinin sauka a filin jirgin saman Diori Hamani ita ce hujjar da Lamine Zeine ya ce kungiyar CEDEAO ta sanar a matsayin abin da ya hana jami'anta halartar wannan zama.
Da ma dai tun a jajibirin wannan zama wasu kungiyoyin kawancen Kungiyoyin Front Patriotique masu goyon bayan majalissarr CNSP suka tare a wurare akalla 3 a birnin Yamai da ke kan titi mai zuwa fadar shugaban kasa daga filin jirgi da nufin bayyana wa tawwagar da ECOWAS za ta turo cewa 'yan kasa ke da maganar kayyade wa'adin mulkin rikon kwarya.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5