Hukumomin Kiwon Lafiyar Dabbobi Sun Ba Da Sanarwar Bullar Annobar Murar Tsuntsaye Ta H5N1 A Nijar

Ma'aikatan kiwon lafiya a Hong Kong suke yanka kaji da ake zaton sun kamu da murar tsuntsaye.

Tuni dai wannan al’amari ya haddasa mutuwar dubban kaji, abin da ya sa mahukunta suka dauki matakai don dakile yaduwar cutar.

NIAMEY, NIGER - Tun a tsakiyar watan Disamban da ya gabata ne aka fara ganin alamomin annobar ta cutar murar tsuntsaye H5N1 a birnin Yamai da gundumar Bouza ta jihar Tahoua inda ake hasashen wasu kajin da aka shigo da su daga Najeriya ne mafarin wannan al’amari, da tuni ya haddasa mutuwar dubban kaji, kamar yadda babban darektan kiwon lafiyar dabbobi na kasa Dr. Abdou Issiako ya bayyana wa manema labarai.

CUTAR MURAR KAJI

Masu gidajen kiwon tsuntsaye sun bayyana damuwa a game da bullar kwayar cutar ta H5N1 sakamakon dimbin asarar da wannan annoba ka iya janyo wa fannin dake matsayin madogarar mutane da dama.

Domin takawa wannan masifa burki hukmomin kiwon lafiyar bisashe sun fara daukan matakan gaggauwa.

A yanzu dai hukumomi sun hana shigo da tsuntsaye daga ketare kamar yadda matakin ke shafar masu kasuwancin tsuntsaye daga wannan Jiha zuwa waccan to amma ‘yan rajin kare hakkin masaya irinsu Alhaji Maman Nouri na kungiyar ADDC WADATA na ganin tsaurara matakai akan iyakoki it ace hanya mafi a’ala.

Sama da tsuntsaye 100,000 ne suka mutu ko aka kashe a bara a Nijar sanadiyar annobar cutar murar tsuntsaye, lamarin da ya haddasa wa masu gidajen kiwon tsuntsaye asarar dimbin kudade, koda yake gwamnati ta biya diyya ga wadanda abin ya rutsa da su inji babban darekta Dr. Abdou Issiako, kamar yadda a yanzu haka aka dauki matakin rage asara ga irin wadanan mutane.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Kiwon Lafiyar Dabbobi A Nijar Sun Bada Sanarwar Bullar Annobar Murar Tsuntsaye H5N1.mp3