Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shawo Kan Masassarar Tsuntsaye a Kano


Gonar Kaji
Gonar Kaji

Gwamnati ta taka rawar gani a yunkurin ta na kawar da yaduwar annobar masassarar tsuntsaye a jahar kano.

A wani yunkuri na kawar da barkewar annobar cutar kaji, an hallaka kimanin kaji miliyan guda a jahar Kano inda abin yafi kamari a kokarin da hukumomi suka yi na durkusar da cutar bayan da aka sami rahotannin barkewar ta a jahohi goma sha takwas.

Gwamnati tarayyar Najeriya ta hannun ministan lamuran noma ta sha alwashin tallafawa masu kiwon kajin da annobar ta shafi gonakin su, ta kyasta bada tallafin dubu daya da dari uku ga kowacce kaza guda daya, ya zuwa yanzu dai gwamnatin ta biya tallafi ko diyyar kaji guda dubu dari a matsayin kashin farko kamar yadda wani mai kiwon kajin ya bayyana a jahar kano.

Hukumar raya kasashe masu taso wa ta Amurka wadda aka fi sani da USAID a karlkashin shirin ta na bunkasa harkokin noma a Najeriya, ta bada horo ga kwararrun da ke bincike da kariya daga yaduwar annobar cutar ta masassarar kajin.

Dr Ganiyu Abubakar shine daraktan kiwon lafiyar dabbobi a ma'aikatar gona ta tarayyar Najeriya yayi karin bayanin cewar dole ne kokarin kawar da cutar domin kauce hatsarin shigar ta jikin dan adam. Bayan haka kuma dole ne mu tallafawa masu kiwon tunda kiwon kaji wata hanya ce ta ciyar da al'umma.

Kawo yanzu dai babu wani rahoton da ke nuna bullar cutar a fadin jahar ta kano baki daya.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

An Shawo Kan Masassarar Tsuntsaye a Kano -2'33"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG