Murar tsuntsaye ta sake bayyana a Kamaru. Musamman a yammacin ƙasa inda aka fi kiwon kaji. Gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai don gudun yaɗuwar cutar a sauran jihohi.
Shekaru biyar kenan Kamaru bata ji ɗuriyar annobar murar tsuntsaye ba. Bana kuma ta sake ɓullowa ne musamman a jahar Yamma, Jahar da tafi ƙarfafa kiwon kaji a kasar.
Da haka ne ministan kiwo Dr Taïga ya rattaba hannu kan wata doka da ta tanadi matakan gaggawa na hana yaduwar cutar a kasa. Daga cikin su, an haɗa da "ƙidaya dukan wuraren kiwon kaji da aka tabbatar da cutar murar tsuntsaye, da kawar da waɗannan kaji daga doron ƙasa ta hanyar yanka, sannan a ƙona su, kuma a binne su tare da tallafin jami'an kula da lafiyar dabbobi", da jami'an tsaro.
Bugu da kari, Ministan kiwon Lafiyan ya ba da umarnin ƙarfafa tsaro a wuraren kiwon, tare da hana shigar duk wani wanda ba shi da izini, yayin gudanar da ayyukan daƙile kwayoyin cutar.
Makiyayan suma sun fara ɗaukan wasu matakai kamar yadda suka bayyana a hirar wani jami'i da Muryar Amurka. Yace, “A yanzu mun haramta duk wata ziyara cikin akurkin kajinmu. Duk ma'aikacinmu da zai shigo ko zai fita daga wurin aiki sai mun tabbatar da an fesa masa sinadaran kashe ƙwayoyin cutar na riga kafi.”
Waɗansu kuma sun kawo ƙorafi kan tsanancin waɗannan matakai inda suka ce gwamnati zata durƙufar musu tattalin arzikinsu bayan ba ta kawo musu isashen taimako wurin haɓaka kiwon kaji.
Waɗannan matakai, gwamnati tace ta ɗauke su ne da nufin kiyaye sashen kiwon kaji na gida, wanda yake ƙoƙarin farfaɗowa daga wannan cutar da ta bayyana a shekarun baya. Wanda ya sa makiyaya suka yi asarar kimamin biliyan 16 FCFA, a cewar Hukumar Kula da kiwon Kaji ta Kamaru (Ipavic).
Makiyayan da suka fi asara a wannan lokacin sune na jahar yamma, wanda suke bai wa ƙasar kashi 80% a fannin kiwon kaji.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: