Isar da bukatar samun rakiyar jami’an tsaro ita ce hanya mafi a’ala da ya kamata irin wadanan kungiyoyi su bi a yankunan da kawo yanzu ke da wuyar shiga a cewar mahukunta a wata sanarwar da magatakardar ofishin gwamnan jihar ya fitar.
Yankunan da hukumomin jihar ta Tilabery suka saka a matasyin masu jan fenti wato wadanda cike da hadura sun hada da hanyar Tera zuwa Balleyar da hanyar Torodi zuwa Makalondi da Ouallam zuwa Banibangou da hanyar Ayorou zuwa Inates da Ouallam zuwa Banibangou da Sinegodar da Say zuwa Tamou sakamakon tsanantar ayyukan ‘yan ta’adda. Abinda ke zama hannunka mai sanda ga kungiyoyin agaji.
Shugaban kungiyar Action For Humanity Dr. Zirbine Abbas ya nuna damuwa game da makomar al’umomin irin wadanan yankuna.
Yace al’umma ba ta damar zuwa gonaki alhali ana lokacin shirye shiryen fara ayyukan noman damina , haka kuma akwai wadanda ba sa iya komawa garuruwan da suka fito. Abin nufi matsalar rashin samun agaji za ta zo ta karu akan matsalar tsaro. Akan haka ba abinda za a ce sai dai a kara nanata kiran gwamnati ta kara matsa kaimi a yaki da ‘yan ta’adda don samarda tsaro.
Rukuni na biyu na wadanan hanyoyi shi ne wanda hukumomi suka gindaya wa matafiya sharadin neman rakiyar jami’an tsaro galibinsu daga karfe 8 na safe zuwa 4 na la’asar. sun hada da hanyar Filingue zuwa Abala da Ouallam zuwa Managize da Tilabery Torodi da Ballayara zuwa Banibangou da Gotheye Zuwa Tera da Abala zuwa Sanam.
Masanin sha’anin tsaro Abass Moumouni na ganin wannan mataki tamkar wani mafarin haddasa yanayin rudani ne.
To sai dai a rukuni na 3 na karshe na hanyoyin zirga zirgar jihar ta Tilabery hukumomi sun ayyana cewa ba wata barazana ko miskalazarratan akan hanyar Tilabery zuwa Yamai da hanyar Tilabery zuwa Ouallam da Tilabery Filingue da Tilabery Gotheye da Tilabery Ayorou da Tilabery Say da hanyar Tilabery zuwa sassan iyakarta da jihar Dosso.
Jihar Tilabery makwafciyar Mali da Burkina Faso ta tsincin kanta cikin halin tashin hankali sakamakon lalacewar al’amura a wadanan kasashe duk da matakan da gwamnatin Nijer ke dauka da kuma a dai gefe daukin sojan da kasashe aminnai ke cewa suna bayarwa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5