Jihar Tilabery na fama da aika aikar ‘yan ta’adda da ‘yan bindigar da ke satar dabobi da karbar haraji wani lokaci har da kisan fararen hula.
Rahotanni daga karkarar Sanam ta gundumar Filingue a jihar Tilabery na cewa dakarun rundunar Almahaou dake sintiri a wannan yanki da hadin guiwar jami’an tsaron Garde Nationale ne suka kwace wani rukuni na rakumman kimanin 27 a hannun ‘yan bindiga lokacin da suke kokarin ketara iyaka zuwa kasar Mali.
Daya daga cikin shugabanin al’ummar karkarar Sanam Alhaji Lawali ya yi min bayani a game da wannan al’amari, inda ya ce jami’an tsaro sun zo da wasu rakumma a nan wajen mu, sai dai bamu sani ba ko rakumman na mutanen Nijer ko na wasu ‘yan kasar waje bamu iya ganewa ba.
Domin tantance mamallaka wadanan rakuma hukumomi sun ba da dama a ziyarci cibiyar kula da harakar huji ta garin Sanam inda aka ajiye su.
Lawali ya kara da cewa an basu gayyata a matsayin su na shugabannin al’umma don su ga rakumman ko su san tantance ko wadanne iri ne.
Gundumar Filingue kamar sauran sassan jihar Tilabery na fama da aika aikar ‘yan ta’addan arewacin Mali yankin da tun a shekarar 2012 ya fada cikin yanayin tabarbarewar tsaro. dukkan matakan da gwamnatocin Nijer da Mali ke cewa suna dauka da hadin guiwar rundunonin kasashe aminnai abin ya ci tura.
Ga dai rahoton Souley Moumouni Barma daga birin Yamai: