Kungiyoyin ‘yan jarida sun fara nuna damuwa kan makomar kafafen yada labarai masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar.
Fargabar na zuwa ne bayan da hukumomi suka dakatar da shirye-shiryen wani gidan rediyo da talbijin mai zaman kansa da ke birnin Yamai.
Hukumomin sun dakatar da kafar yada labaran ce, jim kadan bayan wata hira da aka watsa da wani lauya mai sukar lamirin gwamnatin ta Nijar, a cewar shugabannin kafar yada labaran.
An watsa hirar ce kai-tsaye a gidan rediyo da talbijin na Labari.
Mukaddashin shugaban tashar, Hima Garba, ya tabbatarwa da Muryar Amurka aukuwar wannan lamari.
Tuni dai wannan lamari ya janyo fushin kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida a kasar ta Nijar, wadanda suka ce ba a bi ka’ida ba.
“Wanda aka zaga shi zai je ya kai kara a hukumar sadarwa wacce ake kira CSA, ita ce ke da ‘yancin ta tuntubi wannan gidan rediyo ko na talbijin,” ta dauki mataki akansa. Inji daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida, Jallo Bubakar.
Ya zuwa yanzu, hukumomin na Nijar ba su fadi dalilin da ya sa aka rufe tashar a hukumance ba.
Amma da wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya tuntubi hukumar CSA mai sa ido kan harkokin yada labarai, Kakakinta, Moussa Muhammad Murtala ya ce sai a taron hukumar na wata-wata za a ta da wannan batu na rufe tashar ta Labari.
Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5