Gerard Collomb ministan tsaron cikin gida na Faransa ya kammala ziyararsa a garin Agadez cikin jamhuriyar Nijar.
Ministan ya samu rakiyar 'yan majalisun dokokin kasarsa su takwas da jakadan kasar Faransa a jamhuriyar Nijar da masu bashi shawara da ministan tsaron cikin gida na Nijar din Muhammed Bazoum.
Ministan ya je Agadez ne domin tattaunawa da hukumomin bariki da na gargajiya da kungiyoyin farar hula da na mata da matasa da duka masu ruwa da tsaki akan kwararar bakin haure.
Gwamnan jihar Agadez Malam Sadu Sanuti ya yabawa kasar Faransa bisa kokarin da ta keyi na tabbatar da tsaro cikin kasar Nijar. Ya kira ministan da su ci gaba da tallafawa kasar Nijar musamman jihar Agadez domin tabbatar da kawo zaman lafiya a kasar.
Shi ko ministan na Faransa cewa ya yi kwararar bakin haure na kawowa yankin kudi saboda ya baiwa matasa abun yi ta hanyar safarar bakin haure. Ya ce yakamata a farfado da tattalin arzikin jihar domin matasan da suka bar harkar safarar bakin haure saboda bin dokar da ta haramta sana'ar.
Tarayyar Turai ta yi alkawarin tallafawa matasan Agadez da yanzu suka rasa ayyukan yi sanadiyar dokar da ta haramta safarar bakin haure.
Sakataren ofishin gwamnan jihar ya ce kasar Faransa ta yi alkawarin tallafawa jihar. Kawo yanzu cikin matasa dubu shida da suka daina safarar bakin haure 250 kacal suka ci moriyar tallafin kasar Faransan.
Rahoton Haruna Mamman Bako nada karin byani
Facebook Forum