Kungiyar kasa da kasa mai bada agaji ta Red Cross,ta fara horas da jami'an jihar Touha domin sanin aikin ba da agaji.
Horon na zuwa ne a karkashin wata yarjejeniya da ofishin ministan tsaron Nijar da kungiyar Red Cross ta duniya da suka kulla tun shekarar 2012.
Alhaji Musa, wakilin kungiyar Red Cross, ya ce da horaswar tana da sauki, amma aiwatar dashi shi ne matsalar. Ya kira masu horon da masu daukan horon da su mayar da hankali akan shirin, domin ba da agajin gaggawa ga mabukata.
Lokacin da gwamnan Jihar Touha Malam Musa Abdulrahaman ya bayyana irin taimakon da kungiyar Red Cross ke kawowa jiharsa, ya ce a shekarar 2017 kungiyar ta baiwa sojoji 120 horo akan sanin mutuncin dan Adam, da girmama shi, da yadda yakamata a bashi agaji.
Haka ma kungiyar ta wayarwa wasu sojoji 60 kai lokacin da yankin ke fama da matsanancin harkokin tsaro.
Jami'ar Touha ta horas da dalibai 200 akan bada agaji. Ta kuma ba da kayan anfanin gida. Kungiyar ta kuma taimakawa 'yan gudun hijira ta basu damar magana da iyalan su ta woyar tarho sau 858 ba tare da sun biya ba.
Gwamnan ya ce kungiyar ta kuma taimaka wajen samar da ruwan sha a garin Ikra, lamarin da ya sa ya mika godiyar kasar Nijar a madadin Shugaban Kasa Mahammadou Issoufou.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani
Facebook Forum