A jamhuriyar Nijar jami'an tsaro sun dauki lokaci suna kwashe duwatsun da matasa suka datse hanyoyi dasu, da kone konen tayoyi domin nuna rashin jin dadinsu akan matakin hana zanga zanga da zaman dirshan da wasu kungiyoyi suka shirya, domin yin tur da dokar haraji dake cikin kasafin kudin kasar na bana.
Kafin akai ga wannan, jami'an tsaro sai da suka yi awan gaba da shugaban wata kungiya Musa Cangari, yayinda yake kokarin shiga ofishinsa. Hajiya Ramatu Soli na cikin abokan tafiyar gwagwarmayar, ta ce bata samu ta yi magana da Musa Cangari ba, kuma bata san abun da suke tuhumarsa dashi ba.
Akan ko gawagwarmayar ta mutu ke nan, Hajiya Ramatu Soli ta ce yanzu ma aka fara domin mutum daya aka kama cikin su dubu.
Baicin Musa Cangari, jami'an tsaron sun cafke shugaban wata kungiya Ali Idrisa, da Nuhu Arzika na kungiyar NPCR, sai kuma wani lauya mai zaman kansa wadanda tuni aka garzaya dasu makarantar 'yan sanda.
Tuni 'yan siyasa suka yi tur da lamarin da suke gani ya sabawa kundun tsarin mulkin kasar. Alhassan na kungiyar 'yan siyasa na cewa kundun tsarin mulkin kasa ne aka taka dalili ke na suka fito su yaki abun da suka kira haramtaciyar dokar kasasfin kudi.
Sai dai tun a jajiberen zanga zangar hukumomin Yamai suka bukaci kungiyoyin kada su fito saboda da dalilan dake da nasaba da tsaro. Dalili ke nan da kakakin gwamnati kuma ministan al'adu Asumanu Malam Isa, ya ce ba yau ba ne ake bada izinin zanga zanga ko kada a bayar ba bisa ga yanayi.
Magajin garin birnin Yamai ya bada shawara cewa a wannan lokacin akwai matsala ta tsaro saboda haka aka hana zanga zangar.
Souley Mummuni Barma na da karin bayani
Facebook Forum