Taron bikin dai ya mayar da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa uku wadanda suka hada da bude fagen sabuwar shekarar lauyoyi, sai kuma bitar ayyukan da kungiyar ta gudanar a tsaron shekaru 30, da kuma mayar da hankali wajen ganin an kawar da duk wani katsalandan din da fannin shari’a ke fuskanta.
Da yake bayaninsa shugaban kungiyar Lauyoyi, Mounkaila Yaye, yace Imani da matsayin shari’a a tafiyar kasar dimokaradiyya ta kowanne fanni, yasa kungiyar lauyoyi zakulo wannan maudu’i da ake ganinsa tamkar gugar zana ne ga masu tafiyar da al’amura a jamhuriyar dimokaradiyar Nijar.
Gwamnatin Nijar ta ce ba zata yi ‘kasa a gwiwa ba wajen ‘daukan matakan inganta fannin shari’a, kasancewar dimokaradiyya ba zata girku ba muddin ba a baiwa fannin shari’a cikakken ‘yancin gudanar da aikin ta ba.
Taron dai ya samu halartar tawagar lauyoyi daga kasashe takwas mambobin kungiyar UMOA, baya ga wakilan lauyoyin Faransa da na wasu kasashe renon Faransa.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum