Babban daraktan dake kula da sha’anin tsaro a ofishin gwamnan jihar Neja, kanal Maikundi Mai Ritaya, yace mutumin da ake zargin mai suna Na Imam, gwamnatin jihar Zamfara ta dade tana nemansa ruwa a jallo, amma sai a wannan lokaci ne aka samu nasarar damke shi a jihar Neja.
A halin yanzu dai a kwai wasu Shanun satar da yawansu ya kai 500 da aka kama a karamar hukumar Shiroro, amma wasu Fulani da suka fito daga Katsina sunce sunga wasu daga cikin Shanun su da aka sace wanda ba a basu ba.
Gwamnatin jihar Neja dai ta daurawa Kanal Mai Kundi Mai Ritaya alhakin kula da Shanun satar da aka kama, ya kuma bayyana dalilin rashin bayar da Shanun da sauri. Inda yace yana yiwuwa a sami matsala idan akayi saurin bayar da Shanun ga masu shi, domin akan iya baiwa wani kayan wani.
A kwanakin da suka gabata ma rundunar yan Sandan jihar Neja, tace ta samu nasarar cafke wasu muggan barayin Shanun tare da Shanun sata, har ma da wasu muggan makamai kamar yadda kwamishinan yan Sandan jihar Abubakar Marafa, ya tabbatar.
Your browser doesn’t support HTML5