Sakamakon koma bayan kudaden shiga daga asusun tarayya, wadanda gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suke dogaro akai, gwamnatin jihar Nija dake arewacin Najeriya, ta shawarwaci kananan hukumomi da suke jihar, su duba hanyoyin da zasu bi domin inganta hanyoyin samun kudin shiga, kada su dogara kan Abuja kamar yadda aka saba, yanzu hakan ba zai wadatar ba.
Gwamnan jihar Nijan, Alhaji Abubakar Sani Bello yayi alkawarin gwamnatinsa ba zata rike kudaden kananan hukumomi ba karkashin tsarin asusu daya, kamar yadda yake a tsarin mulki. Kuma gwamnatoci da suka wuce ba su yiwa kananan hukumomin adalci ba.
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi Alhaji Gambo Tanko Kagara, yace, a zaman shawarwari da suka yi da Gwamnan jihar kan bukatar su maida hankali kan bukatun jama'arsu.
Ga karin bayani.