Karamar hukumar Gudu ce kadai ba a gudanar da zabe ba, sakamakon rashin bayyanar wani dan takara a takardun jefa kuri’a. haka kuma jam’iyyar ta APC ce ta lashe dukkan kujerun kansiloli 234 daga kananan hukumomi 22 na jihar da aka gudanar da zaben.
To sai dai tuni jam’iyyar PDP mai adawa ta yi fatali da sakamakon zaben. Sakataren jam’iyyar PDP na jihar Sokoto, Kabiru Aliyu, yace, “maganar canji da APC yanzu ya bayyana a fili cewa yaudara ce, jam’iyyar APC ta lalata tsari na dimokaradiyya gaba daya, an hanawa mutane abin da suka zaba an koresu daga runfunan zabe, an cika akwati an kawo yan daba suna saran mutane tare da hadin kan yan sanda da jami’an zabe. to sun kuma dawo da wani abu wadda ko jam’iyyar PDP da tayi shekara 16 tana batayi irin wannan ba.”
To amma jami’iyyar APC ta musanta zargin ta bakin sakataren ta na watsa labarai Sidi Aliyu Lamido, inda yace “Baka hana dan adam korafi, sannan kafin a sa ranar zabe duk wanda yake a jihar Sokoto zai fada maka babu jam’iyyar PDP a jihar, domin mu bamu ma dauke ta ba a matsayin jam’iyyar da zamu fafata tsakanin mu da ita ba….” Sidi Aliyu Lamido, ya tabbatar da cewa an gudanar da gaskiya a cikin zaben da akayi.
Ita kanta hukumar zaben ta nisanta kanta daga zargin kamar yadda shugaban hukumar Usman Abubakar ya bayyana, inda yace anyi amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a kuma duk wanda bai tantance ba to ba a bashi kuri’a ba. ya kuma ce duk wanda bai amince da sakamakon zaben zai iya shigar da kara kotu.
Duk da yake dai an sami karancin masu jefa kuri’a a mafi yawan runfunan zabe, an sami hayaniya a wasu guraren abin da yakai har da baiwa hammata iska.
Domin karin bayani.