Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin Maharba Da 'Yan Banga Ya Halaka Rayuka A Adamawa.


Maharba da Kayan Yakinsu.
Maharba da Kayan Yakinsu.

Al'amarin ya auku ne a karamar hukumar Gombi, lokacinda daya banagaren yake wani taro.

Rundunar 'Yansanda a jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar akalla mutum daya sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin maharba da kuma 'yan banga.

Sassan biyu suna bada adadin wadanda rikicin ya rutsa da su zuwa 7, wasu fiyeda 10 kuma sun jikkata. An kai su asibiti a Yola, fadar jihar Adamawa.

Lamarin ya auku ne a garin Gombi helkwatar karamar hukumar yayin wani taro da wani reshe na kungiyar maharban suka shirya.

Duka sassan biyu suna aza laifin tarzomar akan daya bangare. Kuma suna bada adadin masu sabani da juna.

Kakakin rundunar 'Yansandan jihar DSP Usman Abubakar, yace tuni aka fara bincike kuma duk wanda aka samu da hanu wajen hura wutar wannan rikici, sai fuskanci shari'a.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG