Har ma yace Saudiyar zata taimakawa Najeriyar wajen yaki da miyagun akidu dake fakewa da musulunci kamar yan ta’addar Boko Haram. Ta hanyar komawa koyarwar Alkur’ani da Hadisin Manzon Allah ne za a iya yaki da wannan fitunar ta yan ta’adda, dake addabar kasashen musulmin duniya daban daban.
Al-Turki dai yazo Najeriya ne don gagarumin taron kafa sahihiyar akidar musulunci da wanzar da zaman lafiya da za a gudanar a hadin gwiwar Ahlus Sunnah.
Shi kuma jakadan Saudiya a Najeriya, Fahad bin Abdullah, yace Najeriya na daga gamayyar kasashe 34 da Saudiyya zata jagoranta don yaki da ta’addanci. Haka kuma yace ta’addancin yan ISIS da sauransu dake murkushe zaman lafiyar kasashe, ya sabawa koyarwar addinin Islama.
Shugaban kungiyar Izala na kasa Shiek Abdullahi Bala Lau, “An san gwagwarmaya da halin da Najeriya ta shiga ciki yan shekarun da suka gabata na kashe kashe da zubda jini, da wadansu daga cikin mu suka dauki rigar musulunci suke cewa wannan shine addinin musulunci…..”
Za dai a fara taron gadan gadan ranar 17 ga wannan watan na Maris, wanda zai sami budewa daga shugaba Mohammadu Buhari.