Shugaban hukumar USAID a Najeriya, Michael Harvey, yayi bayani bayan rattaba hannu da gwamnatin Najeriya tayi kan yarjejeniyar raya ilimi a kasar. Bisa ga rahotan hukumar kididdiga ta Najeriyar da ta gano an sami karuwar mata dake shiga makarantu musammam ma a jihohin Arewa.
Mr. Harvey ya nuna farin ciki da yadda yace yayi ran gadi a yankunan arewa inda yaga a wasu guraren Masallatai da Majami’u na samar da waje da akan kafa makarantu, don samawa yara saukin samun ilimi. A cewar Mr. Harvey, “Mu wannan hukumar muna da tsarin kafa wasu yan cibiyoyi masu shigen makarantu a cikin al’umma, da zamu dauki nauyinsu don tabbatar da ilimin ya shiga dukkan lunguna.”
Shugaban hukumar ilimin bai daya na Najeriya, Dakta Sule Dikko, shine ya wakilci ma’aikatar ilimi a wajen yarjejeniyar, da yace ta hanyar bin tsarin kididdigar za a cimma gagarumar nasara.
A nasu bangaren malaman addinin islama na kara taimakawa wajen karfafa ilimin Boko a matsayin halal, don yaki da akidar Boko Haram.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5