Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya kammala ziyarar kwana biyu da ya kai Najeriya inda ya gana da takwaransa na Najeriya Muhammad Buhari.
Shugabannin biyu sun amince zasu jagoranci wani kwamitin kasa da kasa na kasashen biyu na inganta tsarin diflomasiya da cinkayya da harkokin muamala tsakanin kasashen biyu.
Malama Garba Shehu na ofishin shugaban kasar Najeriya ya yi karin haske akan ziyarar ta Jacob Zuma. Yace a ganawar da shugabannin suka yi sun amince da fitar da wata takardar shigowa da ficewa ta kasa da kasa da aka sani da suna biza. Wannan takardar zata ba 'yan kasashen biyu damar shiga da fita kodayaushe ba tare da sake neman izini ba na wasu shekaru da dama.
Akwai yarjejeniyar bunkasa harkokin tsaro tsakanin kasashen da ma wasu harkokin daban.
To saidai Shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa inda daya daga cikin kamfanonin Afirka ta Kudu mai hidimar sadarwa dake Najeriya da aka zargeshi da taimakawa kungiyar Boko Haram wajen kin bin umurnin kasa da rufe duk wata lambar sadarwa da ba'a yiwa rajista ba kamar yadda dokar Najeriya ta tanada.
Cikin watan biyar na wannan shekarar kwamitin zai fara zamansa a Afirka ta Kudu domin fara aiki akan yarjeniyoyin da kasashen suka cimma da suka hada da harkokin noma da hakar ma'adanai.
Ga karin bayani.