Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Jacob Zuma Zai Karfafa Dangantaka Tsakanin Kasashen Biyu


Nigeria South Africa
Nigeria South Africa

Najeriyar na kokarin fadada hanyoyin samun kudaden shigarta

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma na ci gaba da ziyarar kwanaki uku da yake yi a Najeriya a yau Laraba, a wani mataki na kokarin kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu da suka kasance jagora a nahiyar Afrika.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin ‘yan jarida, Malam Garba Shehu, ya ce wannan ziyara ta na da muhimmanci lura da cewa kasashen za su iya amfana da juna ta fannoni daban daban, musamman ma a wannan lokaci da Najeriyar ke kokarin fadada hanyoyin samun kudaden shigarta, kamar a fannin noma da hakar ma’adinai, wadanda fannoni ne da Afrika ta kudun ta yi fice.

Ya kuma kara da cewa shugabannin suna tattaunawa kan batutuwa da suka shafi tsaro musamman a fannin kera makamai.

Wannan ziyara ta Zuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama kan wani batun tsaro, inda shugaba Muhammadu Buhari ya zargi kamfanin sadarwa na MTN da kin katse layukan mutanen da basu yi rijista ba, lamarin da ya yi zargin cewa ya taimakawa kungiyar Boko Haram wajen kai hare-hare.

XS
SM
MD
LG