Wanann ziraya dai na da Muradin duba yadda yan Gudun Hijira ke rayuwa don jawo hankalin al’umma ga tallafa musu. Yan gudun Hijirar dai sun nuna aniyar komawa gida matukar lamuran tsaro suka inganta, yawancin su sun fito ne daga yankin Goza da wasu sassa na jihar Adamawa.
Shin wacce irin mu’amula sukeyi da juna tsakanin mabiya addini da ra’ayoyi daban daban a sansanin. Mataimakin shugaban wannan sansani Alhaji Usman Adamu, ya nuna yadda ake zaman lafiya da walwala tsakanin duk mutanen da ke wannan sansani, ba tare da takurwa kowa ba.
Wasu daga cikin yan Gudun Hijirar sun bayyana irin yadda suka tsinci kansu cikin wannan hali. Ado Adamu na daga yan Bunu Yadi a jihar Yobe dake tallafawa yan Gudun hijirar, wanda shima an kashe ya yansa biyu a fitunar Boko Haram, yace ya dace a tallafa wajen gyara kauyukan da ake sa ran komawa.
Tawagar wakilan Muryar Amurka dai sun zaga a sansanin inda suka ga yan Gudun Hijirar ke ci gaba da yin wasu sana’o’insu musammamma dinki, amma akwai wasu da dama da basa yin komai sai jiran komawa gida.
Domin karin bayani.