Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a ranar Talatar shekaran jiya tsakanin babban lauyan gwamantin Najeriya (Atoni-Janar) Abubakar Malami, da kuma Ministan harkokin wajen Switzerland Didier Burkhalter.
Kudaden dai wadanda suka rage ne daga cikin wadanda tsohon shugaban kasar a karkashin mulkin soji Janar Sani Abacha ya boye ne a bankunan kasar. Garba Shehu yace suna sa ran dawowar kudin zuwa gida nan ba da dadewa ba.
Sai dai mafi yawancin ‘yan Najeriya na fargabar da wuya ayi amfani da kudin ta hanyar da talaka zai mora, domin kuwa suna nuna cewa ko kason farko na irin wadannan kudade da aka taba cetowa Najeriya, ba talakan da ya mora domin kuma sun sake batan dabo ne.