Hukumar Kwallon Kafa Ta Ghana Ta Kori Kocin Black Stars

Chris Hughton kocin Ghana Black Stars da aka kora

Hukumar kwallon kafa ta Ghana (GFA) ta kori kocin tawagar Ghana Black Stars, Chris Hughton daga aiki ba tare da bata lokaci ba.

KUMASI, GHANA - Hukumar GFA a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 23 ga watan Janairu, 2024 a shafinta na yanar gizo, ta ce, “GFA na son sanar da cewa an sauke Chris Hughton daga mukaminsa na babban kocin tawagar kasar ba tareda bata lokaci ba.

Majalisar zartaswa ta kuma dauki matakin sauke mataimakansa wato Technical Team daga mukaminsu Inji sanarwar.

Hukumar kwallon kafar Ghana ta kara da cewa nan da kwanaki masu zuwa "za ta samar da taswirar hanya kan makomar Black Stars."

Tuni dai Chris Hughton ya dauki alhakin rashin nasara da Ghana ta yi akan Mozambique a minti na karshe wanda ya sa Black Stars ta fice daga wani mataki na rukuni a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Tawagar Black Stars dai sun tashi daci 2-2 da Mozambique a wasansu na karshe na rukunin B a filin wasa na Olympics da ke Abidjan a daren ranar Litinin.

Sakamakon ya bar Black Stars a matsayi na 3 a rukunin, da maki 2 kacal.

Da yake magana a taron manema labarai bayan wasan, Hughton ya ce, "Na dauki alhakin rashin nasararmu a wannan wasan kuma na yarda cewa sakamakona tare da Black Stars bai yi kyau ba."

-Hamza Adam