Wasan na Senegal da Zimbabwe dai ya yi zafin gaske ba kamar yadda aka yi hasashe ba, kafin a minti na karshe Senegal din ta sami zura kwallo ta hanyar fanariti.
Sadio Mane ne ya zura mata kwallon da ya ba ta nasarar doke Zimbabwe din da ci 1-0 a wasan na su na farko na rukunin B.
Kasar ta Senegal dai na cikin kasashe na gaba-gaba da ake hasashen za su iya lashe gasar ta bana, kasancewar yanzu haka ita ce ta farko a nahiyar Afirka, a jadawalin mafifitan kasashe ta haujin tamaula na hukumar kwallon kafar duniya wato FIFA.
To sai dai tauraruwar ta bata haska sosai kamar yadda aka zata ba a wasan nata na yau da Zimbabwe, bayan da ta sami tafiya gasar da ‘yan wasa 17 kacal a maimakon 28, sakamakon matsalolin da suka shafi cutar coronavirus da kuma raunuka.
A daya wasan rukunin na B, Guinea ta doke Malawi da ci 1-0, wanda ya ba ta damar samun maki 3, daidai da Senegal.
A rukunin C kuma kasar Ghana ta sha mamaki, bayan da Morocco ta doke ta da ci 1-0, yayin da kasashen Gabon da Comoros suke can suna fafatawa a halin yanzu.
A jiya Lahadi ne dai aka soma gasar ta bana tare da kasashe 24 a karon farko, inda a wasan farko, mai masaukin baki wato kasar Kamaru ta yi waiwayen baya ta doke Burkina Faso da ci 2-1.
Burkina din ce dai ta soma zura kwallo a ragar Kamaru a wasan nasu na rukunin A, to amma kuma kasar ta Kamaru ta sami bugun fanariti har sau 2, wadanda kuma duk ta sami zura kwallo a cikinsu.
Haka a jiya din, Cape Verde ta yi galabar doke kasar Habasha da ci 1-0 a rukunin na A.
A gobe Talata ne za’a yi karon battar karfe tsakanin Najeriya da Masar, inda kuma Sudan za ta kece raini da Guinea Bissau duk a rukunin D, bayan wasan farko ta rukunin E tsakanin mai rike da kambin gasar wato Algeria da Saliyo.