Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta Nuna Damuwa Kan Yawan Kisan Fulani A Najeriya

Wani Bafulatani Da Shanunsa

Yayin da al'ummomi ke ci gaba da kokawa kan matsalar rashin tsaro a Najeriya, masu fafatukar kare hakkin bil'adama na nuna damuwa a kan yadda al'ummar Fulani ke shan tsangwama da rasa rayukansu a wasu wurare na kasar

A baya duk lokacin da aka samu rahoton kai hari ga wata al'umma mutane kan saukar da haushi ga kabilar Fulani da ke zaune kusa da su, saboda akasari su ne aka fi zargi da hannu ga harin ta'addanci.

Sai dai daga baya, abin ya sauya zuwa kai wa Fulani hari ko da ba'a samu rahoton kai harin ta'addanci ba, abin da ya sa al'ummar Fualnin ke ta kokawa.

Masu fafatukar kare hakkin bil'adama na nuna damuwa a kan wannan batun, kamar yadda jami'in gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama Ibrahim Adamu Tudun Doki ya shaida ma Muryar Amurka.

Haka kuma Dr. Abubakar Usman Ribah fitaccen malamin addinin Musulinci ya bayyana damuwa da abin da ya gani da idonsa, a kan wannan batun.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bakin kakakin ta a Sakkwato ta ce a can baya an yi ta samun wadannan matsalolin, kuma yanzu haka ma rundunar ta karba bukatar shugabannin kungiyar Fulani ta Miyetti Allah domin ta ji korafe-korafensu.

Wani mai bincike a kan lamurran rashin tsaro a yankin Arewacin Najeriya D. Murtala Ahmad Rufa'i ya ce a farko sun yi ta ankarar da mahukunta a kan yiwuwar samun irin wannan matsala.

A jihar Sakkwato kananan hukumomin da lamarin ya fi kamari sune, Illela, Gwadabawa, Silame da Dange Shuni, kuma ko a jihar Kebbi an samu wannan matsalar lokacin da Lakurawa suka kai hari a garin Mera inda daga baya mutane suka saukar da haushi kan Fulanin dake zaune tare da su shekara da shekaru, hakan kuma ya yi ta faruwa a wasu jihohin Najeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama Ta Nuna Damuwa Kan Yawan Kisan Fulani A Najeriya.mp3