Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI, ta kama wani Ba Amurke da take zargi da shirya kai harin ta’addanci wani fitattcen wurin yawon bude ido a birnin San Francisco ranar Krisimeti.
Jiya Juma’a jami’an suka sanar da cewa sun kama Everitt Aaron Jameson mai shekaru 26 da haihuwa na garin Modesto dake jihar California a farkon makon nan.
Jameson ya fadawa wani jami’in FBI da yayi shigar burtu cewa ya shirya zai kai hari wajen ziyarar masu yawan bude ido a birnin San Franscisco, ta hanyar tayar da bam da kuma budewa mutane wuta da bindiga mai sarrafa kanta yayin da suke guduwa.
Kamar yadda bayanai daga hukumar FBI suka nuna, Jameson ya zabi wurin da zai kai harin ne saboda ya taba zuwa kuma yasan wuri ne da mutane ke cincirindo. Ya kuma fadawa jami’in FBI cewa babu ranar da ta dace kai harin kamar ranar Litinin ranar Krismeti. Kuma bai tsara wata hanyar tsira ba don a shirye yake ya mutu.
Jami’an FBI sun bincike gidan Jameson inda suka gano wata takardar wasiyya, hade da manyan bindigogi da karamar bindiga da albarusai. Cikin takardar wasiyyarsa yayi Allah wadai da amincewa da birnin kudus a matsayin babban birnin Isra’ila da shugaban Amurka Donald Trump yayi.