Da gagarumin rinjaye Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da kudurin kin yadda da shawarar da Amurka ta yanke ta amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isira’ila da kuma shirin bude ofishin jakadancinta a wurin.
“Amurka za ta rika tunawa da wannan ranar da aka aunata a Babban Zauren MDD, saboda kawai mun yi amfani da ikonmu na kasa mai diyauci,” abin da Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta fada ma zauren da ya cika makil kenan a gabanin kada kuri’ar.
“Za mu tuna a duk lokacin da aka sake kiranmu mu bayar da gudunmowa mafi yawa a MDD, kuma za mu tuna a duk lokacin da kasashe da dama su ka zo wurinmu neman taimako, kamar yadda su ka saba yi akai-akai, don su samu na biya wani abu ko kuma su yi amfani da tasirinmu wurin cimma wata bukata,” a cewarta.
Dama Falasdinawa ne su ka bukaci wannan taro na gaggawan da aka yi jiya Alhamis kan wannan daftarin da kasar Masar ta gabatar.
Kuri’ar ta Babban Zauren MDD ta biyo bayan hawa kujerar na-ki da Amurka ta yi ranar Litini a Kwamitin Sulhun MDD kan wani daftari makamancin wannan da sauran mambobin Kwamitin 14 su ka goyi bayansa.
Matsayin Babban Zauren MDD din ya sake jaddada matsayin Birnin Kudus na Birni Mai Tsarki, a matsayin inda aka kwana a kokarin sasanta Falasdinawa da Isira’ilawa; kuma ya yi watsi da duk wani mataki na canza matsayi ko kuma yanayin Birnin Kudus din.
Facebook Forum