Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Juyawa Amurka Baya


Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Babban Zauren Majalisar ta yi watsi da matsayar da Amurka ta dauka cewa Birnin Kudus shine babban birnin Isra’ila yayin da jakadiyar Amurka a Majalisar ta yi gargadin cewa Amurka za ta dauki mataki kan kasashen da suka ki amincewa da wannan matsayar, abin da ta ke kallo a matsayin raini.

“Lallai Amurka ba za ta manta da wannan ranar da aka wareta a cikin zauren majalisar ana sukarta saboda ta yi amfani da gashin kanta a matsayin kasa mai ‘yanci. Lallai zamu tuno da wannan ranar a lokacin da za a zo neman gudummuwarmu a matsayin kasar da ta fi kowa bayarwa ga majalisar. Haka zalika zamu tuno da wannan ranar a lokacin da kasashe da dama da suka saba zuwa neman taimakonmu don bukatar kansu,” Inji Jakadiyar Amurka, Nikki Haley.

Tayi wannan maganar ne kafin kada kuri’ar amincewa da matsayar, inda kasashe 128 suka zabi amincewa da ita, wasu kasashe 9 kuma suka ki da wasu kuma 35 da suka kaurace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG