Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya zai kada wata kuri’a kan wani rukuni na takunkumi, da zummar dada tsaurin hanyoyin da Koriya Ta Arewa ta ke bi wajen sayo mai daga kasashen waje, wanda ke taimaka mata wajen haramtaccen shirinta na nukiliya.
Wannan takunkumin da ke tafe martani ne ga kaddamar da wani sabon makami mai linzami mai iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata da Koriya Ta Arewa ta yi ran 28 ga watan Nuwamba, wanda ta yi wa lakabi da Hwasong-15, wanda ta ce na iya jefa makamin nukiliya a ko ina a Amurka.
Wannan shi ne karo na uku da Koriya Ta Arewa ta kaddamar da makami mai linzami mai iya tafiya daga wata nahiya zuwa wata a 2017; kuma shi ne karo na 20 da ta kaddamar da makami mai linzami a shekarar ta 2017.
Amurka ce ta tsara daftarin sannan ta cimma jituwa da China akansa. Jiya Alhamis aka raba wa dukkan sauran mambobin kwamitin sulhun da zummar kada kuri’ar yau Jumma’a da karfe 1 pm.
Daftarin, kamar yadda Muryar Amurka ta gani, na da manufar rage yawan man da Koriya Ta Arewa ke shigo da shi a halin yanzu, ta yadda ba zai wuce ganga miliyan 4 ba a shekara. Daftarin zai yi la’akari ne kawai da batutuwan da su ka shafe lalura kuma ko shi dinma sai da amincewar Kwamitin Sulhu na MDD din.
Facebook Forum