Hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria(EFCC)ta sake kamo manyan jami’an Bankunan nan su goma sha daya.
Hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Nigeria(EFCC)ta sake kamo manyan jami’an Bankunan nan su goma sha daya. Domin tuhumarsu da aikata sabbin laifukan handama da babakere.
Jami’in dake magana da yawun hukumar ta (EFCC,sunce sabuwar tuhumar da yanzu ake masu ta hada da halatta kudin haram da satar kudaden jama’a da aka bayar ajiya a Bankunan su. Wata kotun Nigeria ta saurari karar da aka kai gabanta sannan ta bada belinsu.
A shekarar 2009 ce babban Bankin Nigeria (CBN)ya bada umarnin korarsu daga aiki sanan tayi belin Bankunan da kudi da yawansu ya kai Dala miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar.