Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban mutane sun kwana a waje a kasar Spain a saboda fargarbar aukuwar karin girgizar kasa


Mutane a garin Lorca na kasar Spain suke kokarin komawa gidajensa bayan da suka kwana a waje a saboda fargabar aukuwar karin girgizar kasa data kashe akalla mutane takwas.
Mutane a garin Lorca na kasar Spain suke kokarin komawa gidajensa bayan da suka kwana a waje a saboda fargabar aukuwar karin girgizar kasa data kashe akalla mutane takwas.

A saboda fargarbar karin girgizar kasa, bayan da wasu tagwayen girgizar kasa sukas hadasa hasarar rayuka a jiya Laraba, duban mutrane sun kwana a waje.

Dubban jama’a a birnin Lorca na kudancin kasar Spain sun kwana a waje saboda suna fargabar karin girgizar kasa bayan wasu tagwayen girgizar kasar da aka yi suka haddasa hasarar rayuka jiya laraba. Jami’ai a yankin Murcia mai farin jinni ga ‘yan yawon bude ido, sun fada yau Alhamis cewa akalla mutane takwas ne girigizar kasar ta kashe, ta rushe gidaje da majami’u da kuma wasu wurare na tarihi. Ba kamar yadda rahotanni daga farko suka bayyana cewa mutane 10 ne suka halaka, yanzu an tabbatar cewa mutane takwas ne su mutu.

Masu aikin agaji sun raba borguna da kayayyakin abinci da kuma ruwa ga mazauna garin Lorca, yayinda ko ina ka duba sai kaga rusassun gine gine da motoci da suka lallace birjit gani a tituna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG