‘Yan Najeriya a jihohin arewa biyu da mummunar fitinar bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ta aukawa sun nufi rumfunan zabe domin zaben Gwamna.
Masu sa ido sun bada labarin cewa mutane basu fito ba sosai a jihohin na Kaduna da Bauchi,duk da baza jami’an tsaro ta ko ina a rumfunan zabe.
Ranar Talata ce aka yi zaben gwamnoni a sauran jihohin Najeriya,amma aka karawa wadan nan jihohi lokaci sabod a su farfado daga tashe tashen hankula na makon jiya.
Wata kungiyar rajin kare hakkin bil’adama tace an kashe akalla mutane 500 a tarzomar da ta biyo bayyana sakamokn zabe da ya ayyana shugaba Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben.
Jam’iyyar PDP ta shugaba Jonathan ce take rike da mulkin jihohin Kaduna da Bauchi, amma tana fuskantar hamayya mai karfi daga ‘yan takarar jam’iyyar CPC ta Janar Muhammadu Buhari.