A kokarinsu na ganin an cigaba da zama lafiya a jihohin Bauchi da Kaduna, shugabannin gargajiya da na siyasa sun yi ta kiraye-kirayen a gudanar da zaben gwamnoni cikin kwanciyar hankali. Su ka bukaci a zauna lafiya bayan zaben ko da wa Allah Ya bai wa nasara a zaben.
Da ya ke magana kan zaben a hirarsu da Halima Djimrao ta Sashen Hausa Na Muryar Amurka, Sarkin Jama’a a jihar Kaduna, Alhaji Mohammed Isa Muhammadu ya bukaci masu kada kuri’a musamman ma a jihar Kaduna su cigaba da zama lafiya da juna koda yaya sakamakon zaben ya kasance. Ya ce shugabanci fa al’amari ne na Allah. Yakan bayar das hi ga wanda ya so ya kuma hana wanda ya so.
Shi ma a nasa bayanan a hirarsu da Halima, Sarkin Kataf a jihar ta Kaduna, Malam Harrison Yusuf Bungon, ya bukaci al’ummar jihar Kaduna da ma Nijeriya baki daya su cigaba da zama lafiya da juna. Ya ce tuni Allah ya riga ya zabe wanda ya ke so tun kafin ma a yi zaben. Don haka ya ce yakamata a gane cewa shugabanci al’amari ne na Allah.
Shi ma da ya ke bayani ga Halima a hirarsu, kwamishinan yada labaran jihar Kaduna, Alhaji Sa’idu Adamu ya ce hukumomin jihar sun kimtsa tsab don gudanar da wannan zaben. Ya ce an dau matakan tsaron da su ka dace. Alhaji Sai’du Adamu bayyana cewa bayanai sun nuna cewa matasan da a baya su ka shiga tashe-tashen hankula sun gane cewa ana amfani ne da su ta hanyar da ba ta dace ba don haka sun dawo daga rakiyar masu son amfani da su.
Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC) ta dage gudanar da zaben gwamnonin jihohin Bauchi da Kaduna daga ran Talata zuwa yau Alhamis ne saboda dalillan tsaro da kuma bukakar shiryawa sosai. A zabukan das u ka gabata an fi samun tashe-tashen hankula a wadannan jihohin.
Rahotanni dai na nuna cewa zaben na zangon karshe bai yi armashi ba kamar na ‘yan majalisar dattawa da na shugaban kasa; kuma an sami zarge-zargen magudi nan da can.